Yau Jumma'a 4 ga wata da yamma, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kama hanyarsa ta dawowa gida bayan da ya kammala ziyararsa a kasar Korea ta Kudu.
Shugaba Xi ya sauka a birnin Seoul, hedkwatar kasar Korea ta Kudu a ranar 3 ga wata, inda ya yi shawarwari da shugabar kasar madam Park Geun-hye, tare da ba da wata sanarwar hadin gwiwa. Yau kuma ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Chung Ui-hwa da firaministan kasar Chung Hongwon. Har wa yau shugaba Xi ya yi jawabi a jami'ar Seoul. Kana ya halarci bikin bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin kasashen Sin da Korea ta Kudu ta fuskar yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.
Wannan ne karo na farko da shugaba Xi ya ziyarci Korea ta Kudu tun bayan da ya zama shugaban kasar ta Sin. (Tasallah)