in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Koriya ta Kudu sun fitar da hadaddiyar sanarwa
2014-07-04 10:45:50 cri

Kasashen Sin da Koriya ta Kudu sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa a ranar alhamis 3 ga wata a birnin Seoul, inda bangarorin biyu suka bayyana cewa, a matsayin muhimman makwabta biyu da ke arewa masu gabashin Asiya, za su raya dangantakar abokantaka irin ta samun bunkasuwa tare, da shimfida zaman lafiya tare, da farfado da Asiya tare, da kuma sa kaimi ga samun albarka a duk duniya tare. Haka kuma kasashen za su kara azama ga bunkasuwar dangantakarsu yadda ya kamata bisa tushen "sanarwar hadin kan kasashen Sin da Koriya ta Kudu don samun makoma mai kyau nan gaba" da kuma wannan hadaddiyar sanarwar da suka daddale.

Sa'an nan bangarorin biyu sun sake tabbatar da tsayayyen matsayinsu na adawa da samun makaman nukiliya a zirin Koriya.

Sin ta sake nanata cewa, kasar Sin kasar ce daya tak a duk duniya, don haka Taiwan wani yanki ne na kasar da ba za'a raba su ba.

A nata bangaren kasar Koriya ta Kudu ta ce, ta fahimci haka tare da cigaba da tsayawa tsayin daka kan cewa, kasar Sin kasa ce daya tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin ita ce halaltaciyyar gwamnati daya tak da ke iya wakiltar kasar Sin a duniya. Haka kuma kasar Koria ta Kudu ta nuna goyon bayanta ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan lami lafiya.

Har ila yau bangarorin biyu sun cimma matsaya daya cewa, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Koriya ta Kudu tana da wata muhimmiyar ma'ana ga bunkasuwar dangantakarsu. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China