Bankin duniya ya yi hasashen dorewar bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara
Wani rahoton bankin duniya ya yi nuni da cewa,makomar matsakaicin bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara zai kasance cikin yanayin da ya dace,inda aka yi hasashen samun ci gaban alkaluman GDP na kashi 4.7 cikin 100 a shekarar 2014.
Rahoton Bankin ya kuma yi nuni da cewa,bunkasuwar za ta karu zuwa kashi 5.1 cikin 100 a shekarar 2015 da 2016,lamarin da zai kai ga bukatar zuba jari a bangaren albarkatun kasa,kayayyakin more rayuwa da aikin gona.(Ibrahim)