Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gargadi 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar CPC da su guji yin sakaci, su kuma gano inda suke da rauni duk da irin yabon da al'umma suke ma jam'iyyar.
Shugaban ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin jajibarin cikan jam'iyyar CPC shekaru 93 da kafuwa, a lokacin wani taro kan yadda za'a inganta tsarin ayyukan jam'iyyar da tabbatar da da'an mambobinta.
Mr. Xi wanda ya yi kiran da a mai da hankali sosai wajen nazarin matsayin jam'iyyar ya bukaci mambobinta da su fahimci hadarin da'a da jam'iyyar ke fuskanta kamar ware kanta daga sauran al'umma, da kuma cin hanci da rashawa. Abin da, in ji shi, ya kamata a dage wajen ganin an tafiyar da jam'iyyar ta hanya mai tsanani.
Yananin aikin jam'iyyar ya dogara ne a kan da'an da mambobinta ke da shi wajen tafiyar da ita, don haka ya bukaci mahukunta da su karfafa aikinsu karkashin sa idon jama'a, domin kyautata ayyukan jam'iyyar CPC yadda ya kamata. (Fatimah)