Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika AU a ranar Alhamis game da babban taro karo na 23 da wannan hukuma ta gudana a birnin Malabo, tare da bayyana cewa, kasar Sin na nuna goyon baya sosai ga hadin kan Afrika da tsarin samun makoma mai kyau, da ma dunkulewar wannan yanki.
Abokantaka tsakanin kasar Sin da Afrika na da alfanu da kuma kasancewa tushen samun cigaba ga mutane biliyan 2,3, tare da taimakawa cigaban hadin kai da dangantaka tsakanin kasashen dake samun cigaba, in ji mista Xi.
Duk da sauye-sauyen da ake samu a duniya, kasar Sin za ta cigaba har kullum wajen taimakawa abokin da ba ya da karfi, kuma kasar Sin, abokiyar huldar nahiyar Afrika ce ta gaskiya, in ji mista Xi. (Maman Ada)