in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam`iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomin jihar Kano dake arewacin Najeriya
2014-05-19 15:24:23 cri

A ranar lahadi 18 ga wata aka kammala bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar 17 ga wata a jihar Kano dake arewacin Najeriya, inda jam`iyyar APC ta lashe dukkannin kujerun kansiloli sama da 800 dana shugabannin kananan hukumomin jihar 44.

Zaben wanda shugabannin jam`iyyar PDP suka ayyana a matsayin wanda yake cike da kura kurai, ya kasance zakaran gwajin dafi a shirye shiryen zaben shekarar 2015.

Jam`iyyar APC ta `yan Hadaka da ta kunshi tsoffin jam`iyyun ANPP da CPC da AD ita ce ta lashe dukkannin kujerun.

Akwai jam`iyyu da dama da suka shiga zaben, amma a wani rahoto na hadin gwiwa da jam`iyyun suka fitar a daren lahadin nan, sun amince da sakamakon zaben.

To sai dai kuma a tattaunawar dana yi da shi ta wayar tarho, daya daga cikin manyan shugabannin jam`iyyar PDP a jihar Kano Alhaji Musa Dan birni ya ce basu amince da sakamakon ba, domin kuwa a cewar sa Gwamnan Kano ya yi amfani da karfin iko wajen aikata magudi.

Ya ce akwai wurare da dama da ba a bari an gudanar da zaben ba amma kuma aka sanar da sakamako, a don haka kamar yadda ya shaida mini suna jiran jagoran su ambasada Aminu Wali ya dawo daga kasar faransa domin su tattauna akan matakin da za su dauka.

Da na tambaye shi irin matakin da yake jin za su dauka, ya gaya min cewa ba za su kai kara kotu ba, domin kuwa kotun ma ba za ta yi masu adalci ba, amma za su samo hanya mafi dacewa wajen kwato hakkin su.

Ana sa ran rantsar da sabbin shugabannin ne a ranar 29 ga wannan wata na Mayu, lokacin bikin cikar gwamnan jihar Kano shekaru 3 kan gadon mulki.

Babu dai wani rahoto na rikicin da ya barke bayan sanar da sakamako, amma rundunar `yan sanda ta jihar Kano ta bukaci `yan siyasa musamman wadanda jam`iyyar su ta samu nasara dasu dakatar da gudanar da shagulgulan murna har zuwa wani lokaci domin kaucewa tashi hatsaniya.(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China