in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran kasashen Afirka su taka rawar gani a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Brazil
2014-06-12 20:20:55 cri
Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ce ta ji dadin yawan kasashen Afirka da za su fafata a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a fara a Brazil, inda ta bayyana tabbacin cewa, kasashen za su fito da sunan nahiyar.

Mataimakin shugaban kamfanin sadarwa da watsa labarai na kasar(GCIS) Nebo Legaobe, ya ce ana kara samun kasashen nahiyar Afirka da ke shiga manyan gasanni,kuma a shirye suke su rika tallafa kulob-kulob din nahiyar,inda ake fatan za su taka rawar gani fiye da gasar shekarar 2010 da ta gudana a kasar Afirka ta kudu.

Kasashen Najeriya, Ghana, Algeria, Cote d'Ivoire, da Kamaru ne ke wakailtar nahiyar a gasar ta bana da ke gudana a kasar Brazil.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China