An ce bisa ka'idar hukumar kwallon kafa ta duniya, Costa na da damar ya bugawa Sifaniya wannan gasa, duk kuwa da kasancewar sa daya daga 'yan wasan da suka bugawa kasar Brazil wasannin sada zumunci biyu. Sai dai a hannu guda ana ganin 'yan kasar ta Sifaniya ba su baiwa hakan cikakken goyon baya ba.
Har wa yau kalaman da kocin kasar Brazil Felipe Scolari ya yi cewa, yana da nufin sanya Costa cikin jerin 'yan wasan Brazil, idan Costan bai zabi ya bugawa Sifani wasa ba, sun dada rura wutar cece-kuce da ake yi game da shawarar da Costa ya yanke.
Sai dai a daya bangaren Costa ya shaidawa 'yan jaridu cewa, babu wani koci da ya gayyace shi in banda kocin Sifaniya, wanda ya bukaci su tattauna, ya kuma nuna damuwar sa game da makomar dan wasan, don haka Costa ke cewa ba ya da-na-sani, kan wannan shawarar da ya yanke ta bugawa Sifani kwallo. Amma fa duk da hakan ya bayyana cewa zuciyar sa na tare da Brazil.
'Ina jin kewar Brazil, wannan ba abu ne da zai canza ba, kasancewar an haife ni a Sergipe dake tsakiyar kasar ta Brazil, kuma ko a gidana dake birnin Madrid, al'adun Brazil na ke yi, wanda hakan shi ma ba zai canza ba" in ji Costa. Har ila yau wannan dan wasa ya bayyana cewa, muddin Sifani ba ta samu nasarar lashe gasar ba a bana, to yana fatan Brazil da dauki kofin.
A baya dai an rika bayyana shakku kan ko Costa zai iya buga wannan gasa ko a'a, duba da raunin da ya sha fama da shi, wanda ya hana shi buga cikakken wasan karshe ga kulaf din sa na Atlentico Madrid, a gasar cin kofin zakarun turai ta bana wadda Real Madrid ta lashe.
A yanzu haka dai an ce Costa na cikin koshin lafiya, ya kuma alkawarta baiwa kungiyar kasar ta Sifaniya cikakkiyar gudummawar da ta dace domin samun nasarar ta.