Sai dai fa daya daga 'yan wasan ta Dinijel Pranjic ya samu rauni, a yayin wasan da kungiyar ta yi da Australiya a juma'ar da ta gabata, wasan da Crotian ta lashe da ci daya da nema.
Dan wasan Crotian Nikica Jelavic ne dai ya jefa kwallo a zaren Australiya cikin minti na 58 da fara wasan, wanda hakan ya jefa farin ciki zukatan magoya bayan kungiyar kasar ta Crotia, koda yake a hannu guda raunin da Pranjic ya ji ya sanya magoya bayan kungiyar damuwa matuka. An ce dai mai yiwuwa ne Pranjic ya kaza buga wasu daga cikin wasannin, ko ma daukacin wasannin da Crotian za ta buka baki daya.
Kocin kungiyar ta Crotia Niko Kovac dai ya bayyana cewa, zai dakata ya ga yadda jikin dan wasan zai kasance kafin daukar wani mataki a nan gaba. Kuma ko da yake bangaren dama na bayan kungiyar tasa na iya fuskantar barazana sakamakon raunin da Pranjic ya samu, Kovac ya ce rawar da Sime Vrsaljko ya taka a wasan ta nuna zai iya maye gurbin Pranjic.
Koci Kovac ya ce koda yake Austaraliya ba ta kai Brazil karfi ba ta fuskar taka leda, duk da haka wasan da suka buga da ita ya basu damar gwada kwarewar su, gabanin wasan da za su buga da Brazil a ranar farko ta bude gasar cin kofin duniya na bana. Yace 'yan wasan sa sun shirya fafatawa da Brazil, kuma muddin sun taka kwallo yadda ya kamata, babu wani abu da za su ji tsoro. Daga nan sai ya yi fatan 'yan wasan na sa zasu taka leda yadda ya kamata, kamar yadda suka yi bayan hutun rabin lokaci a wasan su na sada zumunci da kasar Australiya.
Bugu da kari kwatar kai da Brazil ta yi da kyar daga hannun Serbia, yayin wasan sada zumunci da ta buga, inda aka tashi Brazil din na da kwallo daya Serbia na nema, ya karawa Crotia karfin gwiwar tinkarar Brazil din ba tare da wata fargaba ba.