Mr Ouyang ya bayyana cewa, wurin da kamfanin Sin ke aiki na kusa da yankin tsibiran Xisha na Sin, tazarar dake tsakanin wurin da tsibirin Zhongjian ta kai mil 17 kawai a teku, kuma tazarar dake tsakanin wurin da iyakar kasar Vietnam ta kai kimanin mil 150 a teku don haka bai kamata Vietnam ta dasa shinge kan ayyukan kamfanin Sin a yankin teku na kasar Sin ba.
Bayan haka, Ouyang ya kara da cewa, sau da yawa kasar Sin ta bukaci Vietnam da ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yankin kasa da kuma ikon kulawa na Sin, ta daina dasa shinge ga ayyukan kamfanin Sin a wurin, tare da janye jiragen ruwa da ma'aikatanta daga wannan yankin teku. Amma Vietnam ta kara tura jiragen ruwa zuwa wannan yanki, su rika yin karo da jiragen ruwa na Sin. A game da wannan batu, Sin ta nuna rashin jin dadinta da babbar murya, kuma ta dade tana jaddada bukartar ga Vietnam da ta daina irin wannan ayyuka ta janye jiragen ruwa da ma'aikata duka nan take.(Fatima)