Kasar Kenya wadda ke matukar amfana daga sashen yawon shakatawa, sakamakon kasancewarta daya daga cikin kasashen Afirka da suka yi fice a wannan fanni, na samun koma baya sakamakon kalubalen tsaro dake addabar ta yanzu haka.
Bisa wani rahoto da kwamitin kula da harkokin yawon shakatawa na duniya ya fitar, an ce yanayin tsaron kasar ta Kenya na kara tsananta, sakamakon hare-haren ta'addanci da kasar ke fuskanta a kai a kai.
Har wa yau wannan rahoto ya yi nuni da cewa, yawan karuwar mizanin tattalin arziki na GDPn kasar a sashen yawon shakatawar na shekarar 2013, ya kai dalar Amurka biliyan 5.4, adadin da ake zaton karuwarsa da kashi 3.1 bisa dari kacal, adadin da bai kai ya kawo ba, sakancewarsa a matsayi na hudu a jerin kasashe 5 na mambobin kungiyar raya gabashin Afirka, da ke kunshe da kasashen Tanzaniya, da Kenya, da Uganda, da Ruwanda, da kuma Burundi.
Rahoton ya kuma ci gaba da cewa, matsalar rashin tsaro, ta zama babban kalubale mafi muni ga sha'anin yawon shakatawa a kasar ta Kenya. Inda aka yi hasashen cewa yawan guraban ayyukan yi da ake samu daga wannan sashi zai ragu da kimanin dubu goma a bana kadai. (Danladi)