Shugaban kasar Najeria Goodluck Jonathan ya umurci sojojin kasar da su kaddamar da yaki gadan-gadan da kungiyar Boko Haram domin murkushe barazanar da 'yan ta'addan suke yi.
Shugaban kasar ya bayar da wannan umurnin ne a cikin jawabin da ya yi wa al'ummar kasar na bikin ranar dimokradiyya.
Shugaba Goodluck Jonathan ya jaddada kudurin gwamnati na kare mulkin dimokradiyyar a Najeriya, da kuma tabbatar da hadin kan kasa da samar da zaman lafiya mai dorewa a bangaren siyasa.
Kamar yadda ya ce, gwamnati a shirye take ta yi tattaunawar sulhu da duk wata kungiyar da ke da muradin gaskiya na yin watsi da ta'addanci.
Shugaban kasar ya yi kira a kan 'yan Najeria da su hada kansu, domin samun nasarar yaki da 'yan ta'adda.
Jonathan ya kuma yabawa rundunar sojojojin Najeria a kan sadaukar da kansu da suka yi wajen tunkarar matsalar tsaro, ya kuma bukaci 'yan kasarsa da su jinjina musu maimakon su dinga yin allah wadai da su. (Suwaiba)