in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya salami ministocinsa 9 a wani gyaran fuska
2013-09-12 09:56:40 cri

A ranar Laraban nan 11 ga wata, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sallami wassu ministocinsa guda 9 a wani gyaran fuska a majalissar zartarwarsa, in ji kakakin fadar gwamnatin kasar Reuben Abati a Abuja.

Cikin wadanda wannan sallama ya shafa sun hada da manyan ministoci 6 wato ministan harkokin waje Olugbenga Ashiru, ministan ilimi Ruqayyatu Rufa'i, ministan tsare-tsare Shamsudden Usman, ministan filaye da cigaban birane Ama Pepple, ministan kimiyya da fasaha Ita Okon da ministan muhalli Hadiza Mailafia.

Sai kuma kananan ministoci uku da suka hada da ministan ayyukan gona Bukar Tijjani da na tsaro Olusola Obada da kuma ministan makamashi Zainab Kunchi.

Kakakin fadar shugaban kasar a bayanin da ya yi ma manema labarai ya ce, wadanda aka sauke din za'a maye gurabensu nan ba da dadewa ba.

Da take tabbatar da wannan al'amari, daya daga cikin ministocin da aka sauke, ta muhalli Hadiza Mailafia ta ce, hakan ba zama abin mamaki ba saboda ana sa ran wannan sauyi tun ba yau ba, ta yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya.

Wannan kwaskwarima dai shi ne na farko da shugaban ya yi tun darewarsa mulki a shekara ta 2011, ganin cewa, yana fuskantar adawa daga sauran 'ya'yan jam'iyyarsa ta PDP a kan bukatar da yake da ita na zarcewa a kan karagar mulki karo na biyu a shekara ta 2015.

Wassu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar sun hada da gwamnoni, wadanda a ranar 31 ga watan Agusta suka balle daga cikin uwar kungiya ta PDP suka kafa wata sabuwa karkashin shugabancin Kawu Baraje, tsohon shugaban jam'iyyar na rikon kwarya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China