in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta jinjinawa salon jagorancin shugaba Jonathan
2013-12-20 10:04:11 cri

A jihar Legas, reshen jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ya jinjinawa salon jagorancin shugaban kasar mai ci, don gane da namijin kokari da jam'iyyar ta ce ya yi na karkata akalar kasar zuga ga turba ta gari.

Da yake bayyana sakamakon babban taron jam'iyyar na jiha da ya gudana a Akija ranar Alhamis, shugaban jam'iyyar na jihar ta Legas Tunji Shelle, ya ce, gwamnatin shugaba Jonathan ta kai kunyarta.

Mr. Shelle ya kara da cewa, a ko da yaushe 'yan adawa ba za su rasa abin fada ba, sai dai a hannu guda ayyukan da gwamnatin mai ci ke yi na sauye-sauye masu ma'ana, za su ci gaba da kasancewa ta garkuwa ga masu sukar lamirinta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China