Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan, ya salami ministocin gwamnatinsa 4, a wani mataki da fadar gwamnatinta ce na da alaka, da aniyar cimma manufar kawo sauyi a kasar.
Wata majiya daga fadar shugaban kasar, ta tabbatar da sauke ministocin yayin zaman majalissar zartaswar kasar na ranar Laraba 12 ga wata. Majiyar ta kuma ce, ministocin 4 sun hada da ta ma'aikatar lura da sufurin jiragen sama Stella Oduah, da na ma'aikatar harkokin 'yan sanda Caleb Olubolade.
Sauran sun hada da ministan ma'aikata mai lura da yankin Niger Delta Godsday Orubebe, da kuma karamin minista a ma'aikatar kudi Yerima Ngama.
Har ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance ko korar ministocin, na da alaka da batun zargin da ake yi, na tsoma hannun wasu jiga jigan gwamnatin kasar mai ci, cikin harkokin da suka jibanci cin hanci da rashawa ba.
Tuni dai shugaban Najeriyar ya dade yana nanata cewa, gwamnatinsa, sam ba za ta lamunci duk wani mataki na saba dokokin gudanar da ayyukan hukuma ba. (Saminu)