in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeriya ya kama rashin lafiya a Landan na Ingila
2013-11-22 10:22:45 cri

Kafofin yada labarai na Nigeriya sun sanar da cewa, shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yi fama da rashin lafiya jim kadan da isarsa birnin Landan na kasar Ingila, abin da ya sa bai iya halarta bude taron 'yan kasuwa da masu zuba jari da ya je musamman ya aiwatar ba.

Kafar yada labarai ta Ingila BBC ta ce, shugaban 'dan shekaru 56 da haihuwa ya samu kulawar likitoci kuma yanayin shi bai yi tsanani ba.

Jonathan dai ya isa kasar Ingila ne a ranar Laraban nan don halartar taro na 'yan kasuwa da masu son zuba jari na kwanaki uku, da zummar jawo ra'ayin su zuba jari a kasar.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta bakin kakakinsa Rueben Abati da aka fitar ya tabbatar wa jama'ar kasar cewa, yanayin jikin shugaban ba mai tsanani ba ne, kuma ya riga ya samu sauki sakamakon duba shi da likitoci suka yi, suka kuma shawarce shi da ya huta na 'yan kwanaki.

Shugaba Goodluck Jonathan da ya hau karagar mulkin kasar a shekara ta 2010, a da an shirya zai koma gida ne a ranar Asabar, amman yanzu sanadiyar 'dan jiyar nan da ya yi, ba'a san ranar da zai koma ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China