in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NAM ta yi kira da a yi wa MDD garambawul a Algeria
2014-05-29 12:47:39 cri

Taron ministocin kungiyar kasashe 'yan ba ruwanmu NAM na 17, ya yi kira da a yi wa kwamitin tsaro na MDD. garambawul kamar dai yadda aka yi wa wasu hukumomin tattalin arziki da na kudade na duniya garambawul.

A cikin jawabinsa na bude taro, firaministan kasar Algeria, Abdelmalek Sellal ya yi kira a kan mambobin kungiyar kasashe 'yan ba ruwanmu da su tattara dukanin karfinsu domin yi wa kwamitin tsaron MDD garambawul.

Sellal ya kuma yi kira a kan 'ya'yan kungiyar da su kunshi kasashe 120, da su ci gaba da hada karfi wuri guda domin murkushe ta'addanci a duniya wanda ya shafi kasashe da dama.

A jiya Laraba ne taron ya kammala ranar taronsa ta farko a Algiers, inda aka mai da fiffiko a kan al'amura da suka hada da yaki da ta'addanci, da kuma yaki da laifukan ketare iyakokin kasashe, kasashe da kuma yi wa MDD garambawul.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yaba da kokarin da kungiyar kasashen 'yan ba ruwanmu take yi, wajen sasanta rikice-rikice da kuma murkushe matsalar talauci a duniya.

Ban ki-moon wanda ya yi jawabi ta kafar na'urar bidiyo, ya kuma kara da cewar, kungiyar NAM ta kasance tana kare muradai na duniya da suka hada da girmama 'yancin dan'adam, da kuma tabbatar da cewar, dukanin mutane da kasashe daidai suke da juna.

Ban ya kuma bukaci kasashen da su ci gaba da kokari wajen fuskantar kalubale na canjin yanayi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China