Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya mika sakon farin cikinsa ga kasar Algeriya a bisa nasarar da ta samu ta gudanar da zaben shugaban kasa a cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ban Ki-moon, ya bukaci kasar ta Algeriya da ta hada gwiwa domin karfafa tsarin damokradiyya a kasar.
Babban sakatare din ya kuma mika murnarsa ga jama'a da gwamnatin kasar Algeriya a game da yadda ga baki daya aka gudanar da zaben na shugaban kasa, kamar dai yadda wata sanarwa da kakakin Ban Ki-moon ya gabatar.
Sakamakon zaben ya nuna cewar, shugaban dake rike da akalar mulkin a kasar Abdelaziz Boutflika ya lashe zaben a karo na hudu da fiye da kashi 81.53 bisa dari na kuri'un da aka kada, a zaben kasar, wacce ke arewacin Afrika, a inda kuma babban 'dan takaransa a zaben Ali Benflis shi ne ya zo na biyu da fiye da kashi 12.18 bisa dari na kuri'un da aka kada. (Suwaiba)