Wakilai da masana mahalartar taron sun ba da shawarwarinsu game da ma'anar yin gyare-gyare game da tsarin gudanar da ayyukan gwamnati, da matakan da za a dauka wajen yin gyare-gyare, da matsalolin da ake fuskanta yanzu, da dai sauransu.
Mataimakin direktan kwamitin kula da tsarin gwamnatin tsakiya na kasar Sin kuma mataimakin shugaban kwamitin nazarin aikin yin gyare-gyare game da tsarin gudanar da ayyukan gwamnati na Sin Wang Feng ya ce, yayin da gwamnatin ke canja ayyukansu, kamata ya yi a canja tunaninsu, sannan kuma, a gudanar da hakikanin matakai bisa tunaninsu, don gudanar da aikin yin gyare-gyare ga tsarin gudanar da ayyukan gwamnatin yadda ya kamata.(Bako)