in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron tattaunawa tsakanin Sin da kasashen yammacin Asiya da na arewacin Afirka
2014-05-29 10:46:55 cri
Da yammacin jiya Laraba ne aka kammala taron tattaunawa, tsakanin Sin da kasashen da ke yammacin Asiya da na arewacin Afirka, taron da hukumar kula da cudanya da kasashen waje, ta kwamitin tsakiya na JKS, da hadin gwiwar gwamnatin lardin Zhejiang suka dauki nauyin shiryawa.

Yayin taron da aka yiwa lakabi da "kishin zuci domin kyakkyawar makoma", mataimakin shugaban sashen kula da harkokin kasashen da ke yammacin Asiya da arewacin Afirka, na hukumar kulda da cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na JKS Jiang Jianhua, ya bayyana cewa, an samu nasarori uku a gun taro, ciki har da batun kara fahimtar juna, da inganta hadin gwiwa, da kuma zurfafa zumunci dake tsakanin sassan.

Mahalartar taron sun gabatar da jawabai game da fasahohin kasashensu, a fagen gudanar da harkokin siyasa, tare da musayar ra'ayi kan tsarin raya kasa, da na samar da bunkasuwa, da yin kwaskwarima, da gyara tsare-tsare da dai sauransu. Matakin da zai kara samar da fahimtar juna, game da yadda za a raya kasar Sin, da kasashen dake yammacin Asiya da ma na arewacin nahiyar Afirka.

Ban da wannan kuma, mahalartar taron sun gabatar da burin samun bunkasuwa, ta hanyar yin kwaskwarima, da kuma mai da wanzar da zaman lafiya a matsayin tushen cimma wannan buri.

A halin yanzu dai, adadin 'yan kasuwa daga kasashen dake yammacin Asiya, da na arewacin Afirka, da ke zuwa birnin Yiwu na kasar Sin don sayen kayayyaki, ya zarta mutum dubu 100, kana fiye da dubu 4 na zaune a birnin. Baya ga hukumomin cinikayya, da kamfanonin hadin gwiwa da aka kafa a birnin, wadanda suka zarce 1100. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China