in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya halarci shagalin murnar ranar Afirka da jakadun kasashen Afirka a Sin suka shirya
2014-05-24 16:41:26 cri
Jiya Jumma'a 23 ga wata, memban majalisar gudanarwa ta Sin, Yang Jiechi ya halarci shagalin murnar ranar Afirka da jakadun kasashen Afirka a Sin suka shirya.

A cikin jawabinsa, Yang Jiechi ya taya murna ga kasashen Afirka da jama'arsu, inda ya ce, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan hanyar karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka cikin dogon lokaci. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan shugabannin Sin sun kai ziyara a kasashen Afirka a kai a kai cikin shekarar da ta wuce, wannan ya nuna cewa, sabuwar gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kwarai kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka. A nan gaba, Sin za ta ci gaba da kokari tare da kasashen Afirka, da zummar zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a duk fannoni, da ciyar da sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare kuma, jakadan Mauritania a Sin ya karanta sakon murnar shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka a wannan karo, kana shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould Abdel Aziz. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China