A lokacin ganarwa su Mr Wang ya ce, yanzu ana cikin yanayin tangal-tangal a Syria don haka Kamata ya yi bangarori daban daban na Syria su dora muhimmanci kan al'umma da kasar, su tsagaita bude wuta tun da wuri.
Ministan yayi kira da su sa kaimi ga yunkurin siyasa mai dorewa, a kokarin tabbatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2139 a duk fannoni, ta yadda za a cimma burin daidaita matsalar Syria a siyasance tun da wuri.(Fatima)