Sai dai makomar samun bunkasuwa ba da karfi duk da cewa yunkurin karo na hudu na watanni uku a shekarar 2013 da ya janyo adadin bunkasuwa an kiyasta shi da shekara da kasha 3.8 cikin 100, in ji gwamnar babban bankin kasar Afrika ta Kudu, madam Gill Marcus a cikin wata sanarwa mai fituwa a cikin watanni uku-uku.
Hasashen bunkasuwar tattalin arzikin da bankin ya kiyasta 'yar raguwa, daga kashi 2.8 zuwa 2.6 cikin 100 a shekarar 2014, kana daga kashi 3.3 zuwa 3.1 a shekarar 2015.
Ja da bayan wannan hasashe na da nasaba da dogon yajin aiki a bangare harkar ma'adinan Platine da kuma matsalolin rashin samar da watur lantarki, in ji madam Marcus.
Lalacewar yanayin tattalin arzikin kasar ya zo a lokacin da rashin shugabannin kamfanonin kasar ke karuwa. Adadin ci gaban da aka samu a karo na hudu na jerin watanni uku a shekarar 2013 ya samu jagora bisa ga karfin bunkasuwar da aka samu a bangaren masana'antun kere-kere, bayan wani ja da baya a watanni uku da suka wuce dalilin yajin aiki. A cikin watan Janairu, bangaren kere-kere ya samu adadin bunkasuwa bisa shekara da kashi 2.5 cikin 100. (Maman Ada)