A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar an ce yarjejeniyar wadanda tun da farko aka amince da su a lokacin ganawar sharen fage da aka yi a Ankara babban birnin kasar Turkiyan a ranar Asabar din da ya gabata ya gano wurare mafi muhimmanci da za'a maida hankali a kai da suka hada da ciniki, masana'antu, sufuri, yawon shakatawa, ilimi, kiwon lafiya, shige da fice, kimiyya da fasaha da kuma yadda za'a yi amfani da filayen da ba su da isassun ruwa.
Wani darakta a sashin kula da nahiyar Turai da kasashe rainon Ingila na ma'aikatar harkoki da kasuwancin kasashen waje a kasar ta Kenya Lazarous Amayo ya ce Kenya tana son amfana daga kasar Turkiya a bangaren masana'antunta.
Ita ma mataimakiyar Darekta a bangaren kasuwanci da yarjejeniya na ma'aikatar tattalin arziki na kasar Turkiyan, Gulendam Muge Varol Ilicak ta ce kasarta a shirye take ta bada hadin kai da taimakon da ya kamata ga kasar Kenya ba tare da wani jan kafa ba. (Fatimah)