Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yi kiran kasashe mambobin gamayyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS da su kawo karshen kamfen tayar da hankali da hare-haren kungiyar Boko Haram dake Najeriya, in ji jaridar gwamnatin kasar Daily Graphic a ranar Talata a birnin Accra.
Mista Mahama, kuma shugaban kungiyar dake shiyyar yammacin Afrika a wannan karo, ya bayyana cewa, tsaro da zaman karko a kasar Najeriya suna hada da juna da na sauran dukkan kasashen shiyyar yammacin Afrika.
A cikin wani sako da ya aike wa shugaban tarayyar Najeriya, Goodluck Jonathan, shugaba kasar Ghana ya kimanta wadannan tashe-tashen hankali a matsayin abubuwan da ba za'a rufe ido kansu ba, domin haka ya zama dole a tashi tsaye wajen yaki da kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)