'Yan sandan dai sun ce ana zaton mutanen biyu, mahara ne da ke da niyyar dana bama-baman a birnin Mombasa a wani wurin taruwar jama'a, da nufin halaka fararen hula masu yawa.
Da yake karin haske kan hakan, kwamishinan rundunar 'yan sandan Mombasa Nelson Marwa, ya ce an warware bama-baman da nauyinsu ya kai kilogaram 173 cikin nasara, ana kuma ci gaba da farautar wasu mutane 5 da ake zargi da hannu a shirin kai wannan hari.
Shi ma a nasa bangare shugaban rundunar 'yan sandan lardin Mombasa Robert Kitur, cewa ya yi suna da tabbashin kungiyar Al-Shabaab ce ta yi nufin kai hari da wadannan bama-bamai a wani gini mai tarin jama'a.
Tuni dai aka gurfanar da mutanen biyun da aka kama da bama-baman gaban kuliya, ana tuhumarsu da yukurin aikata kisan kai da kasancewa 'yan kungiyar Al-Shabab, tare da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba. Laifin da mutanen suka musanta aikatawa. An kuma dage sauraron karar tasu zuwa ranar 22 ga watan Mayu. (Saminu Hassan)