Kulob din ya ba Faehrmann karin wa'adi na shekaru 4, a matsayin wata kyautar yabo kan yadda ya nuna cikakken kwazonsa, da kwarewa a kakar wasannin da ake ciki, matakin da ya taimakawa kulob din samun tikitin halartar gasar zakarun turai a kaka mai zuwa.
Darektan kulob din na Schalke Horst Heldt, wanda ya bayyana hakan a madadin kungiyar, ya kuma yabawa Faehrmann kwarai bisa kokarinsa, inda ya ce duk da cewa mai tsaron gidan ya sha fama da jinya a wannan kakar wasanni, a hannu guda ya yi kokarin samun horo, ya kuma koma filin wasa ba tare da wani bata lokaci ba. Ya ce dan wasan ya taka muhimmiyar rawa musamman ma a rabin kakar wasannin ta karshe.
Ralf Faehrmann mai shekaru 25 a duniya, wanda ya tsare gidan Schalke a wasanni 50 da kulaf din ya buga, shi ma ya nuna farin cikinsa bisa ci gaba da kasancewar sa a wannan kulaf na Schalke. Kulaf din da yanzu haka ke matsayi na 3, a teburin gasar Bundesliga, ya kuma dara Leverkusen dake matsayi na 4 da maki 3.