Dadin dadawa, shugaba Xi ya ce kamata ya yi a dora muhimmanci wajen yin kandagarkin nau'oin hadarori daban daban, domin share fage tukuna, ta yadda za a dauki matakai cikin lokaci, a kokarin rage illar da hadurra ke haifarwa.
Baya ga haka, shugaba Xi ya jaddada cewa, muddin ana nemi samun nasara, to ya zama wajibi a kara kokari yadda ya kamata. Ya ce Mambobin JKSjam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, musamman ma shugabannin ta, dole ne su sa ido kan ayyukansu, tare da yarda a sa musu ido, a kokarin samun amincewa da nasarar ayyukansu bisa mutunci da kima.
Bugu da kari a cewar shugaban kasar ta Sin y a ce kamata ya yi a kara ba da horo, da kulawa, da kuma sa ido kan ayyukan mambobinta jam'iyyar a matakai daban daban, domin a samu gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Daga ranar 9 zuwa 10 ga watan nan na Mayu ne dai shugaba Xi ya gudanar da ziyara a birnin Kaifeng, da Zhengzhou da sauransu, inda ya shiga kauyuka da kamfanoni, da manyan tasoshin jiragen ruwan kasa da kasa da dai sauran muhimman wurare, duka dai da nufin yin nazari kan yanayin da ake ciki, na bunkasar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da kuma hanyar yadda ake gudanar da mulkin bisa kula da moriyar jama'a da ake bi.(Fatima)