Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta kara ba da kwarin gwiwa cewar, ta kammala dukanin shirye-shiryen da ya kamata ta yi, domin tabbatar da zaben kasar cikin kwanciyar hakali, da cikakkiyar kariya, tare da ganin cewar kowa ya samu 'yancin taka rawa a zaben.
Ministan rundunar 'yan sandan kasar ta Afrika ta Kudu, Nathi Mthethwa ya fada a Pretoria cewar, yanzu ya kamata su mai da hankali wajen daukar wasu matakai na gwamnati domin tabbatar da an gudanar da zaben lami lafiya.
Afrika ta Kudu za ta gudanar da babban zaben kasar a ranar 7 ga watan Mayu mai zuwa, zaben dai za'a gudanar da shi ne, karo na biyar tun bayan kawar da mulkin nuna banbancin launin fata da aka yi a kasar .
A halin da ake ciki dai akwai rahotannin da ke cewar, an samu barazana na tashin hankali a cikin jami'yyar ANC, wacce ke rike da ragamar mulkin kasar.
Kusantowar zaben na kara haifar da fargaba, hakan ya nuna cewar, ta yiwu tashin hankali zai kawo cikas ga zaben.
A yayin da yake magana a kan tashin hankalin da aka yi, ministan rundunar 'yan sandan kasar Nathi Mthethwa, ya yi gargadi cewar, gwamnati kasar ba za ta lamunta da duk wani salon na tashin hankali da kawo rudani na karya doka da oda a lokacin zaben.
Ministan ya baiwa jama'ar Afrika ta Kudu da gwamnatocin kasashen waje tabbacin cewar, an dauki matakai na tsaro domin tabbatar da an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali, walwala da baiwa kowa 'yancinsa. (Suwaiba)