in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta shirya samun shugaban kasa mace
2014-05-07 10:17:17 cri

Ganin yadda take da yawan wakilai mata a gwamnati da kuma majalissar dokokin kasar fiye da kowane kasa a duniya, Afrika ta Kudu a shirye take ta samu shugaban kasa mace, in ji ministar mata, yara da nakasassun kasar Lulu Xingwana.

Madam Xingwana ta bayyana ra'ayin shugaban kasar Jacob Zuma wanda a ranar Litinin din nan ya ce, kasar za ta iya samun shugaban kasa mace nan ba da dadewa ba.

Madam Xingwana ta ce, furucin shugaba Zuma yana tafiya ne da jadawalin 'yantar da kuma samar da cigaban mata wanda gwamnati take ta kokarin ganin an inganta shi tun a shekarar 1994.

A cikin wata sanarwa da ta fitar kwana daya kafin aje rumfar kada kuri'a na zaben 'yan majalissun dokoki da na gundumomi da za'a yi a Laraban nan 7 ga wata, ministar ta ce, lallai sun amince da cewa, kasar ta shirya samun shugaban kasa mace nan gaba, ta kara da cewa, a zahiri matan kasar Afrika ta Kudu sun nuna a fili cewa, za su iya rike ragamar mulki ko wane iri ne da aka ba su.

A cikin hirarsa da manema labarai a ranar Litinin din da ya wuce a Johannesburg, shugaba Jacob Zuma ya ce, zai goyi bayan zaben mace a matsayin shugaban kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China