Jam'iyyun siyasa a kasar Afirka ta Kudu sun yi alkawarin kawar da duk wani nau'in tashin hankali kafin da kuma bayan zabukan kasar na ranar 7 ga watan Mayu.
Babban sakataren jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Gwede Mantashe ne ya bayyana hakan ranar Laraba, yayin da jam'iyyun siyasa 32 a kasar suka sanya hannu kan wata takardar nuna da'a a garin Midrand da ke wajen birnin Johannesburg domin su nuna kudurinsu na gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.
Ita dai wannan takardar nuna da'a, tana bukatar jam'iyyun ne da su nuna halin ya kamata a lokacin da suke yakin neman zabe, kana su guji tunzura magoya bayansu ko sauran jama'a domin su tayar da hankali. Akwai rahotannin da ke nuna cewa, an sha samun tashin hankalin siyasa a lardunan Gauteng da Kwazulu-Natal.
Bayanai na bayyana cewa, zaben na wannan karo shi ne mafi zafi tun bayan da aka kawo karshen nuna wariyar launin fata a kasar a shekarar 1994, ko da yake jam'iyyar ANC da ke fatan lashe zaben da babban rinjaye, tana fuskantar kalubale kamar zargin cin hanci da kuma gazawar ta wajen magance matsalar rashin aikin yi da matasan kasar ke fuskanta. (Ibrahim)