Zuma wanda ya yi wannan jan hankali a ranar Litinin cikin jawabinsa na bude taron masu ruwa da tsaki kan harkokin cinikayyar nahiyar dake gudana a birnin Johannesburg na kasar Afrka ta Kudu. Ya kara da cewa nahiyar ta Afirka ba za ta samu dunkulewa, da habaka ta fuskar kasuwanci ba, muddin ba a kara kwazo wajen zuba jari, musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa da kere-kere ba.
Shugaba Zuma ya kara da cewa kasashen wannan nahiya na ci gaba da kara himma a inuwar kungiyar AU wajen ganin sun samar da ci gaban da ake buri a wannan fanni. Ya ce akwai tarin riba ga daukacin masu zuba jari da ke fatan sanya jarin nasu a wannan nahiya.
Bisa kididdiga, huldodin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar na samun ci gaba da kaso kimanin 32 bisa dari daga shekarar 2007, kiyasin da ya ninka na ragowar kasashe masu tasowa dake wajen nahiyar, yake kuma kara habaka sama da na ragowar kasashen da suka ci gaba da kaso mai dama. (Saminu Alhassan)