in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin ma'adinan Jubilee a Ghana ya samar da gangar mai miliyan dubu dari
2014-05-06 10:38:06 cri

Kamfanonin dake aiki a Jubilee na kasar Ghana, dake karkashin kamfanin Tullow Oil, sun sanar a ranar Litinin da samar da gangar danyen mai ta cikon miliyan dubu dari a yankin hakar man fetur na Jibulee dake tazarar kilomoita 70 daga bakin gabar wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika.

Yankin Jubilee na kunshe da arzikin da man fetur da gas, inda wasu kamfanoni ke aiki tare a karkashin kamfanin Tullow Oil da aka gano a shekarar 2007, a bakin gabar kasar Ghana kusa da kan iyaka da kasar Cote d'Ivoire.

Gangar man fetur ta cikon miliyan dubu dari, an hako ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu, in ji kamfanin Tullow a cikin wata sanarwa a birnin Accra.

Gangar man fetur ta farko da aka fara hako wa daga wannan yanki, kuma an isa da ita zuwa jirgin ruwan FPSO Kwame Nkrumah a cikin watan Disamban shekarar 2010. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China