in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Ghana sun yi alkawarin habaka dangantakar dake tsakanin su
2014-03-12 11:02:50 cri

Kasashen Sin da Ghana na da burin daukaka matsayin dangantakar dake tsakanin su zuwa wani sabon matsayi a shekaru masu zuwa.

Hakan dai na kunshe ne cikin jawabin da jakadan kasar Sin a Ghanan Gong Jianzhong ya gabatar, yayin ziyarar da ya kaiwa shugaba John Dramani Mahama a fadar sa, domin ban kwana da shi gabanin kammalar wa'adin aikin sa a kasar.

Mr. Gong wanda ke daf da ritaya daga aiki, ya ce, tsahon sama da shekaru 50 ke nan, mahukuntan kasashen biyu suka shafe suna baiwa juna hadin kai da tallafi mai ma'ana, wanda hakan ke nuna irin nasarar da kasashen za su samu tare a nan gaba.

Daga nan sai ya gode wa mahukuntan kasar ta Ghana bisa hadin kan da suka ba shi, yayin da yake gudanar da aikin sa a kasar.

A nasa tsokaci, shugaba Mahama godewa jakadan kasar ta Sin ya yi, bisa namijin kokarin da ya yi, yayin da yake gudanar da aiki a kasar ta Ghana, yana mai cewa, magabatan kasashen biyu sun ba da gudummawar da ta dace, domin aza managarcin harsashen ci gaban kasashen tare.

A 'yan shekarun nan, kudaden hada hadar cinikayyar kasashen biyu sun tasamma dalar Amurka biliyan 5.4. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China