Farashin kayayyaki ya rike matsayinsa na karuwa a kasar Ghana, tare da cimma kashi 14,5 cikin 100 a watan Maris, idan aka kwatanta da na watan da ya gabata dake kashi 14 cikin 100, in ji hukumar kididdiga ta kasar Ghana a ranar Laraba.
Mista Philomena Nyarko, masanin kididdigar gwamnatin kasar ya bayyana cewa, hauhawar farashin kayayyakin abinci tana kashi 8,2 cikin 100 idan aka kwatanta da ta watan Febrairu dake kashi 7,5 cikin 100, alhali kuma hauhawar farashin kayayyaki da ba na abinci ba take kashi 19,2 cikin 100 idan aka kwatanta da ta watan Febrairu dake kashi 19 cikin 100.
Hauhawar farashin kayayyaki da kashi 14,5 cikin 100 a cikin watan Maris na shekarar 2014 dake mafi girma da aka samu a tsawon shekaru hudu da suka gabata, in ji mista Nyarko. (Maman Ada)