in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin da firayin minista Li Keqiang na kasar Sin ya yi a hedkwatar AU
2014-05-05 21:41:09 cri


Salamu alaikum! Ina matukar farin cikin zuwa Addis Ababa, birnin da ake kira hedkwatar siyasar nahiyar Afirka, da kuma zuwa nan cibiyar taron kungiyar tarayyar Afirka wadda ke alamta zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka domin gabatar da jawabi. Ina nuna wa shugaba Zuma da firaminista Hailemariam Dessalegn godiya bisa jawaban da suka gabatar, kuma ina godiya ga shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka Mohamed Ould Abdel Aziz sabo da goron gayyatar da ya ba ni, da kuma yadda kokarin da gwamnatin Habasha da hukumar kungiyar tarayyar Afirka suka yi wajen karbar ziyarata. A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, ina mika wa aminanmu 'yan Afirka gaisuwa da kuma fatan alheri.

Wannan ita ce ziyara ta farko da na kawo nahiyar Afirka tun bayan da na zama firaministan kasar Sin, haka kuma shi ne zuwana na biyu nahiyar. Sinawa masu shekaruna sun tashi suna jin labaran da suka shafi yadda al'ummar Afirka ke kokarin neman 'yancin kansu tare da mai da hankali a kan yadda ake kokarin gina hanyar dogo tsakanin Tanzania da Zambia. A shekaru biyar da suka wuce, na kai ziyara kasar Masar, ga shi kuma yau na kawo ziyara kasar Habasha, inda na fahimci abubuwa da dama da suka zo daya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, ciki har da tarihinsu da kuma aikin da suke sanyawa a gaba na neman ci gaba. Nasarorin da kasashen Afirka suka cimma a sakamakon yadda suke hada kai da juna ya ba mu kwarin gwiwa, kuma yanzu lokaci ya yi da za a kara daga matsayin hadin gwiwar Sin da Afirka zuwa wani sabon mataki, hadin gwiwar da ke da makoma mai kyau. Afirka a zamanin yanzu nahiya ce da ke cikin kuzari, wanda ke taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da tattalin arziki na duniya, kuma a ganina, nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin ginshikan duniya a wasu fannoni uku.

Afirka na daya daga cikin ginshikan duniya a fagen siyasa. Akwai kasashe 54 a nahiyar Afirka, wadanda ke fiye da kashi daya cikin hudu na kujeru a MDD, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a bangaren kiyaye zaman lafiya a duniya. Kasashen Afirka gaba dayansu na kara karfi tare da kara saurin dunkulewa, wadanda ke hada kan juna tare da magana da murya daya a manyan harkokin duniya. A yayin da kasashe masu tasowa ke bunkasa, ya kamata kasashen duniya su saurari muryar Afirka, kuma ya kamata bangarori daban daban su nuna girmamawa ga rawar da Afirka ke takawa. Afirka a yanzu haka ta kasance wani muhimmin bangare da ke kiyaye kasancewar bangarori da dama a duniya da ma huldar dimokuradiyya tsakanin kasa da kasa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China