in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta fara ciniki da kudin Sin RMB
2014-05-02 17:55:39 cri

Kwanaki kadan kafin firaministan kasar Sin Li Keqing ya fara ziyararsa a wasu kasashen dake nahiyar Afirka da suka hada da Habasha, Najeriya, Angola da Kenya, wani shafin yanar gizo mai suna 'Gabashin Afirka' dake karkashin laimar jaridar 'Business Daily' ta kasar Kenya, ya watsa wani labarin cewa, kasar na shirin kafa wata cibiyar musamman inda za a iya ciniki da kudin kasar Sin RMB kai tsaye, lamarin da ya janyo hankalin jama'ar kasar Kenya sosai.

Mwaniki Muthee wani dan kasuwa ne na kasar Kenya, wanda ya kan shigo da babura da kayayyakin babur daga kasar Sin, sa'an nan ya sayar da su a Kenya. Ya yi shekaru 3 yana wannan sana'a, sai dai har zuwa yanzu yana fuskantar wata matsala, kamar yadda ya ce,

"Babbar matsala da ta yi wa harkar cinikayyarmu dabaibai ita ce musayar kudi. Ana bukatar mu canza kudi zuwa dalar Amurka, sa'an nan mu canza dalar zuwa kudin Sin RMB, wannan yana sa mu yi asara sosai."

Hakika wannan matsalar dake addabar Mwaniki, tana damun sauran 'yan kasuwan kasar Kenya da yawa, wadanda ke ciniki da kasar Sin. A nasa bangare, Martin Oloo, wani masanin ilimin hada-hadar kudi na kasar Kenya, ya yi bayani kan wannan batu da cewa,

"Canjin kudi wani babban aiki ne a bangaren ciniki tsakanin kasa da kasa. Samun wata hanyar musayar kudi cikin sauki zai taimakawa 'yan kasuwa ainun. Na san yayin da 'yan kasuwan Kenya da na sauran kasashen Afirka suke ciniki da kamfanonin kasar Sin, suna fatan canza kudinsu zuwa kudin Sin RMB cikin sauri. Ta la'akari da matsayin birnin Nairobi na kasancewa wata cibiyar ciniki, akwai dimbin masu ciniki da kasar Sin a nan."

Yanzu haka tun lokacin da gwamnatin kasar Kenya ta yi shirin kebe wani wurin da za a iya ciniki da kudin Sin, hakan na alamanta cewa 'yan kasuwa irinsu Mwaniki za su iya canza kudinsu zuwa kudin Sin kai tsaye maimakon su canza su zuwa dalar Amurka da farko kafin su sake canza su zuwa RMB. Ta haka, za su kara samun sauki da magance fuskantar hasara.

Hakika dai, tun lokacin kakar bara, wata jaridar kasar Kenya ta ba da labarin kasancewar shirin kafa cibiyar ciniki da kudin Sin a kasar Kenya, abin da a cewarta zai kasance irinsa na farko a duk fadin nahiyar Afirka. Sa'an nan labarin da shafin yanar gizo na Gabashin Afirka ya gabatar a wannan karo, ya nuna fatan ganin ziyarar firaministan Sin a Afirka za ta taimaka wajen kafa wannan cibiya cikin sauri. Duk wadannan labaru, a ganin masu binciken al'amuran duniya, sun nuna yadda kudin Sin ke kara samun karbuwa a nahiyar Afirka, sakamakon samun karuwar ciniki cikin sauri tsakanin bangarorin 2, wato Afirka da Sin.

Idan mun waiwayi shekarun baya, za a ga yadda huldar ciniki a tsakanin Afirka da Sin take dada samun ingantuwa, inda yawan kudin ciniki tsakaninsu ya kai dalar Amurka biliyan 210.2 a shekarar 2013, jamillar da ta karu da kashi 5.9% bisa makamancin lokacin bara. Ya zuwa watan Janairun shekarar 2013, kasashen nahiyar Afirka da suke amfani da kudin Sin yayin ciniki da kasar Sin sun kai 18. Cikinsu kuma, babban bankin kasar Najeriya ya sanar da sanya kudin Sin RMB cikin kudaden musaya a asusun ajiyarta na gida a watan Satumban shekarar 2011. A karkashin wannan yanayi ne, wasu masana na hasashen cewa, idan an kafa cibiyar nan na ciniki da kudin Sin a Kenya, za ta fara taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki da cinikayya a yankin da kasar ke ciki, wannan shi ma zai taimakawa kokarin habaka ciniki da hadin gwiwa da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin.

Dangane da wannan fanni, Marnell Ouma, wanda shi ma ya kasance wani dan kasuwan kasar Kenya dake ciniki da kasar Sin, ya bayyana ra'ayinsa da cewa,

"Wani abin da ya sha bamban da lokacin da shi ne, yanzu kayayyakin kasar Sin sun riga sun shiga cikin kasuwannin kasashen Afirka sosai. Don haka, kafa wata cibiyar ciniki da kudin Sin zai taimakawa yaduwar kudin Sin RMB a kasuwar Afirka, da baiwa 'yan kasuwan kasashen Afirka sauki wajen ciniki da kamfanonin Sin. Duk da cewa darajar dalar Amurka na nan a yadda ta ke, amma yadda ake kara amfani da kudin Sin zai saukaka harkokin cinikayya da ake gudanar tsakanin Afirka da Sin, ta yadda zai sa kaimi ga kara samun ci gaban cinikayya."

A nasa bangaren, masanin ilimin hada-hadar kudi Martin Oloo ya kara da cewa, samun bunkasuwar ciniki tsakanin bangarorin Sin da Afirka, shi ma zai amfana wa sana'o'i daban daban a Afirka, ciki har da sana'ar Otel-otel ko masaukan baki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China