in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya fara ziyararsa a Afirka
2014-05-04 17:09:21 cri
Wannan shi ne karo na farko da Li Keqiang ya ziyarci nahiyar Afirka bayan da ya zama firaministan kasar Sin, kana karo na farko ne ya kai wa kasashen waje ziyara a bana.

Dalilan da suka sa Li ya mayar da nahiyar Afirka a matsayin wurin farko da zai kai ziyara a bana su ne, da farko, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 50 da tsohon firaministan kasar Sin marigayi Zhou Enlai ya ziyarci nahiyar Afirka. Bunkasuwa ta tsawon shekaru 50 ta hada Sin da Afirka tare, har sun zama abu daya. Suna kan sabon mafari ne na raya dangantakar da ke tsakaninsu.

A shekarar bara, sabon shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a wasu kasashen Afirka, inda ya gabatar da ginshikan kalmomi hudu, wato Gaskiya, da Hakika, da Sahihanci da Ainihin hadin gwiwa. Kalmomin da suka kasance tamkar wata babbar ka'ida, da ya kamata a bi lokacin da ake bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Afirka.

Amma ko yaya za a iya aiwatar da wannan ka'ida? kuma yaya za a iya kara kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka a nan gaba? Wadannan su ne muhimman batutuwan da kasashen Sin da Afirka suke fuskanta tare. Ana kuma fatan yayin wannan ziyarar da Li Keqiang ya fara a wasu kasashen Afirka, za a kai ga samun amsar wadannan tambayoyi.

Mr. Zhang Ming, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ne wanda ke kula da harkokin Afirka, ya bayyana cewa a lokacin ziyararsa a kasashen Afirka, Mr. Li Keqiang zai gabatar da sabuwar ka'idar yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a cikin sabon lokaci, kuma kasar Sin za ta tsara wani sabon shiri bisa wannan ka'ida, ta yadda za a iya zurfafa hadin gwiwa, bisa hakikanin halin da ake ciki tsakanin Sin da Afirka a fannonin samar da ayyukan more jama'a, da ayyukan yau da kullum, da masana'antu, da sha'anin kudi, da kiyaye yanayin duniya, da kara yin musayar abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum, da batutuwan shimfida zaman lafiya da tsaro a Afirka.

Wadannan kasashen Afirka 4 da Mr. Li Keqiang zai ziyarta suna gabashi, da yammaci da kudanci na nahiyar Afirka. Don haka ake ganin ziyara ce da firaministan kasar ta Sin zai yi a Afirka gaba daya.

Bisa labarin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, an ce, yayin ziyarar firaministan kasar Sin Li Keqiang a Afirka zai halarci taruruka da bukukuwa sama da 60, ban da wasu shawarwarin siyasa da ganawa, zai kuma kai ziyara a wurare daban daban. A yayin ziyarar tasa a kasar Habasha, firaminista Li KeQiang zai halarci bikin kammala gina wata babbar hanyar mota da wani kamfanin kasar Sin ta yi, sa'an nan, zai ziyarci wani masana'anta da kasar Sin da kasar Habasha suka gina tare, inda zai kuma tattauna tare da 'yan kasuwa sannan ziyarci wadanda suka ci gajiyar tiyatar jinyar yanar ido kyauta da asibitocin kasar Sin suka yi musu.

Hakaza lika, a yayin ziyarar sa a kasar Nijeriya, firaminista Li Keqiang zai halarci babbar taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa da za a yi a Afirka karo na 24,wanda ya zama na farko da wani shugaban kasar Sin zai halarta, a wajen taron,Mr Li Keqiang zai gabatar da jawabi na musamman game da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, bunkasuwar Sin da Afirka cikin hadin gwiwa da kuma ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen duniya da Afirka gaba.

Haka kuma,a lokacin ziyararsa a kasar Angola, firaminista Li Keqiang zai tattauna batun zaman rayuwar sinawa a ketare tare da wasu wakilan kamfanonin Sin dake kasar har ma da wasu wakilan jama'ar kasar Sin dake kasar Angola. Bayanai na nunwa cewa, a halin yanzu, yawan sinawa dake zaune a kasar Angola ya kai kimanin dubu dari biyu, adadin da ya kai kashi daya bisa hudu na yawan sinawa dake kasashen Afirka.

A zangon sa na karshen zayirarsa a nahiyar Afirka, watau kasar Kenya, firaminista Li Keqiang zai ziyarci kungiyoyin matasa masu aikin sa kai na kasar Kenya da ma'aikatan kasar Sin suka hora, sa'an nan zai gana da manema labarai a yayin ziyarar tasa sannan ya dawo gida.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China