in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar farko da firaministan kasar Sin zai kai a kasar Habasha za ta inganta dangantaka a tsakanin kasashen biyu
2014-05-04 17:09:31 cri

A ranar Lahadin nan 4 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa kasar Habasha wadda ke da lakabin "kololuwar nahiyar Afirka", domin fara ziyarar sa ta farko a Afirka tun bayan da ya hau mukamin firaministan kasar. Kafin wannan, yayin da Xie Xiaoyan, jakadan kasar Sin da ke kasar Habasha ke zantawa manema labarai, ya bayyana cewa, a halin yanzu dai, dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Habasha tana matsayi mafi kyau a tarihi, don haka wannan ziyarar ta firaminita Li za ta kara ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu daga dukkan fannoni zuwa gaba.

Masu sauraro, bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Habasha a shekara ta 1970, ana raya dangantakar yadda ya kamata. Musamman ma bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu daga dukkan fannoni a shekara ta 2003, suna ta kara amincewar juna ta fuskar siyasa, da kara hadin kai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da kara cudanyar juna a fannin al'adu da jama'a, kana suna ta tuntubar juna a kan muhimman lamuran duniya da na shiyya-shiyya. Jakada Xie Xiaoyan ya bayyana cewa, an maida kasar Habasha a matsayin zangon farko a cikin ziyarar farko ta Li Keqiang a kasashen Afirka, wanda ya sheda muhimmancin da kasar Sin ta dora kan dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Ana fatan ziyarar za ta samu babban sakamako a fannin hadin gwiwarsu kan tattalin arziki da cinikayya, a kokarin amfana wa jama'ar kasashen biyu. Xie ya kara da cewa,

"Firaminista Li Keqiang zai kai wa kasar Habasha ziyara daga ranar 4 zuwa 6 ga wata bisa goron gayyatar da takwaransa na kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya yi masa, inda shugabannin kasashen biyu za su tattauna kan ci gaban dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu, musamman ma hadin kai a fannin tattalin arziki da cinikayya. Bayanai na nuna cewa a lokacin ziyarar, bangarorin biyu za su daddale jerin yarjejeniyoyi kimanin 17 ko 18, ciki har da yarjejeniyoyin da suka shafi hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya."

A halin yanzu dai, kasar Sin babbar kawa ce ga kasar Habasha a fannin cinikayya, jimillar cinikayya a tsakanin kasashen biyu a shekarar da ta gabata ta kai dala biliyan 2.1. Kasar Sin ta fitar da kananan ababen da ake sarrafawa a masana'antu, kayayyakin fasahohin zamani, na'urori da injuna, da yadi, da magunguna da dai sauransu zuwa kasar Habasha. Haka kuma ta shigo da ridi da karo da fata da kofi daga Habasha. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun hada kansu a fannonin muhimman ayyukan more jama'a da makamashi da masana'antu don moriyar juna.

A lokacin ziyararsa a kasar Habasha kuma, firaminista Li zai ziyarci babbar hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka AU, bisa gayyatar da shugaban kungiyar AU a wannan zagaye kuma shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz, da Madam Nkosazana Clarice Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin kula da harkokin AU suka yi masa, inda Li Keqiang zai gabatar da jawabi kan tsarin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a sabon zamani,a cibiyar ta AU, wadda kasar Sin ta ba da taimako wajen gina ta. Game da wannan, Jakada Xie Xiaoyan, wanda shi ne wakilin kasar Sin a kungiyar ta AU ya bayyana cewa, wannan ziyarar ta firaminista Li za ta kyautata dangantaka a tsakanin Sin da Afirka. Yana mai cewa,

"Wannan ziyara ita ce karo na farko da Li Keqiang zai kai wa kasashen Afirka a matsayin firaministan kasar Sin, haka kuma ita ce wata muhimmiyar ziyara bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci Afirka a bara. Wannan ya sheda muhimmancin da shugabannin kasar Sin ke dorawa dangantaka a tsakanin Sin da Afirka. Na yi imanin cewa, ta ziyarar, za a kyautata dangantaka a tsakanin Sin da Afirka, kuma za a inganta dankon zumunci a tsakanin bangarorin biyu. Haka kuma ina da imanin cewa, tabbas ne ziyarar za ta samu babban sakamako."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China