in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kai da ke tsakanin Sin da Afirka a fannin aikin gona ya samar da babbar moriya
2014-04-30 17:37:14 cri

A 'yan shekarun baya bayan nan, gwamnatocin Sin da na wasu kasashen Afirka sun mayar da inganta hadin kai a fannin aikin gona a matsayin muhimmin fanni da zai iya fadada hadin kansa, suna nuna goyon baya ga hadin kansu a fannonin manufofi da kudade. A cikin wannan yanayi ne, wasu kamfanonin kasar Sin suka gano kyakkyawar dama da ake iya samu ta cimma moriyar juna a fannin zuba jari a aikin gona a Afirka, sabo da haka ne ma suka inganta hadin kai da kasashen na Afirka a fannin raya gonaki, da dasa tsirrai, da fasahohin aikin gona da dai sauransu.

Kamfanin Tiantang, kamfanin kasar Sin ne da ya yi suna a kasar Uganda da ke gabashin Afirka, wanda yake gudanar da ayyuka a fannonin sarrafa bakin karfe, da kirkire-kirkire, da gina gidajen kwana, da sarrafa abinci, da cinikayya. Amma yanzu wannan kamfanin ya canza manyan tsare-tsaren sa na bunkasuwa zuwa raya gonaki. Shugaban kamfanin Tiantang Mista Zhang Zhigang ya yi nuni cewa, aikin gona ya zama babbar makomar bunkasuwar kamfaninsa.

'Raya aikin gona a Afirka ya samu goyon baya daga gwamnatocin Sin da Afirka, jama'ar Afirka suna maraba da hakan, gwamnacotin kasashen Afirka su ma sun nuna goyon bayan su. Gwamnatin kasar Uganda ba ta buga haraji ga na'urorin aikin gona, kuma tana nuna goyon baya a manufofin ta da suka jibanci samar da irrai. Ruwa da gonaki masu albarka a Uganda, sun dasa wani tushe mai kyau gare mu wajen raya aikin gona. A kasar Uganda, da ma daukacin Afirka, raya aikin gona ya zama wata babbar alkibla, bisa ga tallafin da ake samu ta fannonin manufofi, da kudade, da kwararru.'

Dangane da goyon baya da kasar Sin ke nuna wa kasashen Afirka a fasahohin aikin gona, Mista Wu Zhiping dake a matsayin masani, kuma darektan kula da harkokin hadin kai na kudu maso kudanci a tsakanin Sin da Uganda, kana wakilin bangaren kasar Sin, wanda ya taba shafe shekaru da dama yana aikin hadin kai a tsakanin Sin da Nijeriya, na ganin cewa, yayin da tawagogin kwararru a fannin aikin gona na kasar Sin suke bayar da taimako ga kasashen Afirka, su kan bayar da taimako dangane da fasahohi da bayanai ga kamfanonin kasar Sin da ke zuba jari a aikin gona a Afirkan.

'Abubuwan da kasashen Afirka suke matukar bukata a yanzu su ne, samar da ababen more rayukan jama'a a fannin aikin gona. kuma sakamakon bala'in fari dake haddasa yunwa a wasu wurare, taimakon da kasar Sin ta ba su, zai iya taka wata muhimmiyar rawa ga inganta samar da ayyukan more rayuwar jama'a, da kuma gudanar manyan ayyukan tanajin ruwa domin aikin gona. A halin yanzu dai, kasar Sin tana kokarin raya aikin hadin kai na kudu maso kudanci a tsakanin Sin da Afirka a fannin aikin gona. Kasar Sin ta kan tura tawagogi da ke kunshe da kwararru 30 zuwa 50 zuwa kasasahen Afirka, lallai wadannan tawagogin kwararru suna iya karfafa gwiwar kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da aikin gona a Afirka, da wadanda suke shirin zuba jari a aikin gona a kasashen Afirka.'

Hadin kai a fannin fasaha a tsakanin Sin da Afirka a aikin gona, ba kawai ya shafi gabatar da sababbin tsirrai, da fasahohin da suka dace da Afirka kawai ba ne, a'a, har ma da bayar da taimako wajen kara yawan hatsi, da kudin shiga da manoman Afirkan suke samu.

Da aka tabo Magana kan kyakkyawan tasiri da Sin ta yi a Uganda, daga aikin kudu maso kudanci a fannin aikin gona, wakilin bangaren kasar Uganda James Tumwine ya ce,

'Manoman da suka samu moriya suna farin ciki, ganin karuwar yawan hatsin da suka samu, sun kulla dankon zumunci da kwararru a fannin aikin gona, da masana a fannin fasahohi daga kasar Sin. Sun koyi fasahohin dasa tsirrai, da kiwon dabbobi. A wani yanki, manoman wurin ba su taba kiwon kifi ba, amma yanzu sun samu taimako daga kwararrun Sin, sun samu karuwar yawan kifayen da suke kiwo. A wani yanki na daban kuma, manoman ba su taba dasa shinkafa ba, amma yanzu suna amfani da fasahohin dasa shinkafa karkashin taimakon kwararrun kasar Sin, inda a yanzu haka aka fara dasa shinkafa a yankin na su, kuma ake hasashen cewa, nan gaba mai yiyuwa ne yankin zai iya zama daya daga cikin manyan yankunan da aka fi samun yawan shinkafa a nahiyar Afirka.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China