Sannan bisa gayyatar da Mohamed Ould Abdel Aziz, shugaban wannan zagaye na kungiyar kawancen kasashen Afirka AU, kuma shugaban kasar Mauritania da shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma suka yi masa, Mr. Li zai kuma kai ziyara hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa a ran 5 ga watan Mayu.
Bugu da kari, bisa gayyatar da shugaba Klaus Schwab na dandanlin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa ya yi masa, Li Keqiang zai halarci cikakken zama na dandanlin tattalin arzikin kasa da kasa kan Afirka da za a yi a birnin Abuja na Najeriya a ran 8 ga watan Mayu. (Sanusi Chen)