A cikin shirye shiryen bikin baje kolin shayi na kasa da kasa da za'a bude a litinin din 29 ga wata,a Birnin Xinyang dake lardin Henan,tawagar manema Labarai na gidan radiyon kasar Sin CRI karkashin jagoranci Malam Xia Ji Xuan sun ziyarci Gonar shayi na Maojian dake kauyen Bai Long Tang. Wannan gonar tana da girma matuka kuma kamar yadda aka mana bayani akwai kamfanoni da kuma manoma masu zaman kansu da suka mall aiki gonna kin babu na gwamnati ko daya.
Da farko mun ziyarci wannan gona mun ga ganyen shayin a shuke yadda suka isa tsinke bayan shekaru biyu da aka shuka su Ana kula dasu yadda ya kamata karkashin sa idon wadannan manoma,yadda Suke a shuke launukan kore shar yana da matukar ban sha'awa.
Mun je masana'antar da ake sarrafa shayin Inda muka ga ashe aiki ne tukuru bana raggo na,abunda yasa Ma'aikatan ke korafin cewar matasan yanzu basa son Koyon wannan sana'ar. An hora wadannan ganyaye daga danyu shar Zuwa busassu a cikin wani murhu shafaffe na siminti da aka hura wuta ta karkashin sa,wato kamar yadda ake suyar gyada 'yar ruwa ko motsa gemu a kasar Hausa,sannan ana juya shi da wani irin tsintsiya na musamman na tsawon kamar minti biyar Zuwa shidda sannan a juye shi a wani Katon faifai kamar matankadi a sake zuba wani.
Aiki ne na sauri domin idan aka tsaya da juya zai kone tunda murhun yana da tsananin zafi kamar yadda aka bayyana mana muka kuma ganin domin gani ya kori ji.
An gama sarrafa shayi mun kuma sha,dandanon wannan shayi yana da matukar dadi baya da karfi sosai sannan baya da gafi a baki gashi yana da wani irin kamshi na gamsarwa,saura dame masu sauraro shayin Maojiiang ya ci Sunan shi.