in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Fatimah a Xinyang: Ziyarata a Xinyang
2014-04-25 20:49:54 cri

Assalamu alaikum masu sauraronmu da karanta shafinmu na yanar gizo, Ni ce Fatimah Jibril daga nan sashen Hausa na CRI kuma ina maku albishir na jagorantarku zuwa yankin Xinyang dake da cibiya a yankuna biyu wato Shihe da Pingqiao a lardin Henan, yana kuma da yawan al'umma har miliyan 7.8 yana da dadadden tarihi na fiye da shekaru 8,000 wato lokacin daular Xia a karni na 21 zuwa 16 kafin zuwan Annabi Isa (AS) da kuma daular Shang a karni na 16 zuwa 11 kafin zuwan Annabi Isa (AS). A lokacin wannan ziyara da sashin Hausa na CRI zai kai wannan gari, za mu duba rayuwar mazauna wannan garin da galibinsu kabilar Han ne.

Garin na Xinyang yana makwabtaka da lardin Anhui daga gabashinsa, yana kuma makwabtaka da lardin Hubei daga kudancinsa. Xinyang ya taba zama cibiyar hatsi na kasar Sin baki daya a zamanin daular Tang kafin ya dawo ya zama wani gari mai arzikin gaske a tsakiyar kasar Sin.

Wannan yankin a yanzu haka yana rike da kambun samar da daya daga cikin nagartattun shayi 10 da kasar Sin ke nomawa a cikin shekaru da dama, abin birgewa kuma da wannan yankin shi ne yanayin shi a lokacin zafi ba ya tsanani ya kan tsaya kadaran kadaran, ga yalwataccen hasken rana ga isasshen ruwan sama, sannan yana da yanayi hudu wato damina, rani, bazara da sanyi. Sai dai lokacin sanyin yana dadewa amman sanyin ba ya tsanani.

Mazauna yankin sun shahara wajen noman ganyen shayi da aka fi sani da shayi na Xinyang Maojian, da sauran albarkun gona. Ku biyo mu domin samun bayanai, labarai da na kallon hotuna na yankin XINYANG dake lardin HENAN.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China