in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Fatimah a Xinyang: Ziyararmu a dutsen Jigong Shan da tsaffin gidajen mission da shugabanni
2014-04-28 18:31:33 cri

Wannan dutsen yana da tsawon gaske sai dai duk da hakan a gundumar Henan kan shi yazo na 16 yana da tsawon mita 800 a saman ruwa shi wannan dutse yana da wani yanayi na kamanni kamar kaza shi ya sa a ka bashi Sunan jigong Shan wato dutsen kaza.

Yana da tarihi Mai tsawon tun a shekara ta 1903 lokacin mission da kuma turawa na kasashen waje da 'yan kasuwa masu zaman kansu 23 suka zo wajen tare da Gina gidajen su da wajen aiki saboda yanayin wurin yana da ni'imar gaske,ga shi kuma a zagaye ga koramu da tabkuna,ga tsuntsaye da sauran albarkatun halitta.

An maida wajen wurin tarihi da yawon shakawa bayan da turawa suka tafi har yanzu gidajen su na nan an gyara an ziyara,Babban abin birgewa shine a lokacin marigayi tsohon Shugaban kasar Sin Jiang Jie Shi ya taba kafa ofishin sa a wannan wuri na wani Dan lokaci,kuma har ila yau a wannan wuri akwai cibiyar horar da dabarun yaki a lokacin yaki da Japanawa.

Babban Jami'i Mai kula da wannan wuri a yanzu ya mana bayanin yadda ake Kara inganta wajen saboda tarihin da ya kunsa. Misali har yanzu Ofishin tsohon Shugaban kasar na Sin Jiang Jie Shi yana nan da kujerun sa da wayar tangarahon sa,har da teburun rubutu da kujerar sa,da dan kabet daya jera littattafan dubawa na sha'anin mulki...sannan kuma ga wajen karban baki da su butan shayi da kofunan da yayi amfani dasu.

Har ila yau a cikin gidan da Matar shi ta zauna na tsawon kwanaki biyar kacal a matsayin Uwargidan Shugaban kasar Madam Meilin da dakin da ta karbi baki a wannan lokaci har ta rera masu waka tayi rawa da manyan baki saboda shahararriyar mawakiya ce,yana nan an sa mashi suna Meilin Ballroom domin tunawa da wannan jaruma.

A bangaren cibiyar horas da dabarun yaki ga sojojin kasar Sin kuwa shi kanshi wannan cibiya ko ince gidan akwai lunguna da sako sako da kofofin sirri ta yadda in Abokan gaba sun kawo harin za'a bi ta wani kofan a fita,akwai hotunan tarihi da yawan gaske har ma da wata wasika da tsohon Shugaban Sin Mai Girma Chairman Mao Zedong ya Rubuta ma Marigayi Shugaba Jiang Jie Shi,masu karanta shafin mu Zaku ga hotona da muka buga akan shafin na mu.

A gaskiya yadda kasar Sin take mutunta tarihi abin birgewa ne da matukar sha'awa,sannan abin koyi ne ga sauran kasashen musamman masu tasowa domin Tarihi abin alfahari ne ga Dan Adam.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China