in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Fatimah a Xinyang: Bikin shayi na Maojian a Birnin Xinyang
2014-04-27 15:44:28 cri

Birnin Xinyang yana da dadadden tarihi na zaman takewa da albarka tun noma,daya daga cikin su shine ganyen shayi na Maojian,Wanda yazo na daya cikin nagartattun shayin da kasar Sin ke nomawa a shekara ta 1915,kuma abin mamaki har yanzu yana cikin citta tun shayi 10 a duk fadin kasar Sin.

A Dalilin haka muka zo domin halarta bikin shayi na shekara shekara da ake guda a ruwa a wannan birni Inda muka fara Zuwa wani kauye Mai ban sha'awa da ya samu amincewar al'umma game da yanayin shi Mai dadi da sa nishadi. Wannan kauye shine Hao tang,Wanda yake da ni'imtaccen iska Mai Karin lafiya da kuzari saka akin bishiyoyi da shake shuke kore shar. Mun iso wannan kauye da niyyar ziyarar shi tare da tawagar gidan radion kasar Sin na CRI karkashin jagoracin Malam Xia Ji Xuan Mataimakin Shugaban gidan radion gaba daya.

Mun ziyarci cikin kauyen muka ga gidanjensu da wuraren cin abinci da dai sauran su har da makarantar firamari. Abinda ya birgeni a wannan kauye shine suna da abubuwa da dama dake da kamanni da namu na gida wato Afrika koma ince kasar Hausa.

Misali kamar su Randar ruwa,asabari,tukwanen girka,har ma da yin iccen domin girki. Ga koramu da tabkuna ga kaji gida da kuma agwagwi suna ta wanka a tabki,ga karnuka irin na kauye sunyi lamo suna hutawa.ga Yara suna ta tsalle tsalle da adungure a cikin ciyayi suna Jin dadi da annushawa,Iyayen mata suna bare wake a kofan gida Inda suka aje Dan tebur na saida abubuwan bukatun yau da kullum. Musamman Kayan wasan Yara da su 'yar alawa. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China