in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Fatimah a Xinyang: Ganawar magajin garin Xinyang da manema Labarai
2014-04-27 15:46:11 cri

Maganin garin Xinyang ya sanar da kokarin da ofishinsa keyi na ganin an infanta rayuwar mani a shayi ta yadda zasu amfana daga wannan albarkan noma dake kawo alfanu ga yankin da kasar Sin baki daya.

Malam Qiao Xinjiang ya sanar da hakan ne a yau asabar 26 ga wata a Ganawar sa da manema Labarai na gidan radiyon kasar Sin CRI da Suka je wannan yankin domin halarta bikin kasa da kasa na shayin Xinyang karo na 22 da za'a bude ranar lit inion 28 ga wata.

Malam Qiao yace ganin irin martaban da wannan shayi yake da shi a lafiyar jiki da kuma Sunan da yayi a kasashen duniya,ya zama wajibi gwamnati ta Kara bullo da dabaru domin inganta shi,Wanda yanzu haka tana shirya taron bita akai akai da masana na gida da na kasashen waje domin samo hanyoyin da za'a Kara inganta shayin ya tafi Dana zamani.

Ya yi bayanin cewa yanzu haka Ana horas da manoman wannan shayi da dabaru iri daban daban Akan noma da sarrafa shayin musamman ma Matasa domin sana'ar ya bunkasa ya kuma cigaba shekaru da dama masu Zuwa.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China