in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jadadda niyarta dangane da gina zaman lafiya a Afghanistan
2013-06-20 10:29:18 cri

A ranar Laraba, MDD ta nanata niyarta dangane da tabbatar da tsarin kafa zaman lafiya karkashin ikon Afghanistan.

Mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey shi ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambaya dangane da ra'ayin MDD kan batun tattaunawa game da zaman lafiya a kasar Afghanistan.

Del Buey, a yayin ganawar da manema labarai da aka saba yi kullum ya ce, MDD ta dage kan kudurinta na cewar, cimma zaman lafiya a Afghanistan zai samu yiwuwa ne ta hanyar siyasa, kuma MDD na mai ra'ayin cewa, Afghnaistan da kanta ne ya kamata ta jagoranci shirin cimma zaman lafiya bisa kudurin MDD.

Ya ci gaba da cewa, shirin ba da tallafi na MDD a Afghanistan da aka sani da suna UNAMA a shirye yake ya ba da tallafi ga kokarin kafa zaman lafiya da sulhu a kasar, bisa ka'idojin MDD kuma karkashin jagorancin kasar Afghanistan.

A ranar Talata, kungiyar Taliban ta nuna alamun samun ci gaba a kokarin yin tattauanawa dangane da zaman lafiya, inda ta sanar da bude ofishin siyasa a birnin Doha na kasar Qatar. Ofishin nata dake Doha, za'a yi amfani da shi ne wajen samar da bayani dangane da yanayin siyasa a kasar Afghanistan ga kafofin labaru, in ji rahotanni.

A kuma ranar Talatan ne, shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya ce, wata tawagar majalisar kafa zaman lafiya ta kasar za ta je Qatar don tattaunawa kai tsaye da 'yan Taliban.

Shugaba Karzai da sauran shugabannin kasar sun sha yin tayin zaman tattaunawa ga Taliban don kafa zaman lafiya, to amma, kungiyar ta ki amincewa da hakan, inda ta dage cewar, ba za ta yi tattauanawa ba, sai dakarun kasashen waje sun fice daga kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China