Kwamitin tsaron MDD ya yi kira ga daukacin kasashen duniya, da su dukufa wajen daukar matakan hana sake aukuwar kisan kiyashi a daukacin sassan duniya.
Hakan na kunshe ne cikin wani kuduri da ya samu amincewar daukacin wakilan kwamitin 15, yayin zaman tunawa da kisan kiyashin da ya auku a kasar Rwanda shekaru 20 da suka gabata, inda kwamitin ya tattauna batutuwan da suka shafi barazanar da tsaron kasa da kasa ke fuskanta a fadin duniya.
Har wa yau wakilan kwamitin sun bayyana bukatar da ake da ita, ta daukar kwararan matakan dakile aikata manyan laifuka karkashin dokokin kasa da kasa, tare da daukar darasi daga kisan kiyashin da aka yiwa 'yan kabilar Tutsi a kasar Rwanda cikin shekarar 1994.
Bugu da kari kudurin ya yi Allah wadai da duk wani yunkuri, na lullube kisan da aka yiwa fararen hula a Rwanda, yana mai kira ga MDD ta fidda wani shirin ilmantar da 'yan baya, darussan da ke cikin kisan al'ummar da ya auku a Rwanda, a matsayin wata hanya ta dakile sake aukuwar hakan a nan gaba. (Saminu)