Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Laraban nan ya bukaci kasashen duniya da su dauki darasi daga kisan kare dangi da ya abku a Ruwanda shekaru 20 da suka gabata domin daukan matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.
Mr. Ban yana jawabi ne ta bakin mataimakinsa Jan Eliasson a wani taro na musamman da aka shirya a cibiyar majalissar dake birnin New York domin zagayowar shekaru 20 da faruwar wannan bala'in na kasar Ruwanda, abin da ya kawo asarar mutane fiye da 800,000, 'yan kabilar Tutsi da Hutu, ya ce, bai kamata a manta da gazawar da aka yi ba gaba daya wajen hana aukuwar wannan tashin hankali na kisan kare dangi.
Taron da aka yi wa lakabi da "Kisan kare dangi, laifin da ya kamata a dakatar", sashin samar da bayanai na majalissar dinkin duniya da wakilin din din din na kasar Ruwanda a majalissar da kuma kungiyar mai zaman kanta wato Global Centre for the Responsibility to Protect suka shirya tare.
Bayan jaddada hanyoyin da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu za su iya ba da gudunmuwarsu wajen hana faruwar munanan ayyuka, Jan Eliasson ya kuma bayyana cigaban da aka samu a cikin majalissar a wannan fanni da suka hada da shirin dake nuna nauyin da suke da shi wajen ba da kariya da aka amince da shi a shekarar ta 2005 da kuma kwazon ma'aikatar majalissar a wuraren ayyukansu wadanda suke bayar da gargadin cikin sauri, tare da taimakon kokarin ayyukan cikin gida da na waje don ganin hana yaduwar tashin hankali, yana mai ba da misali da kasar Sudan ta Kudu tare da cewa, ya kamata a duba sauran wurare da suka ba da taimako ta hanyar kwazonsu da bullo da dabarun kare mazauna bayan Sudan ta Kudu.
A cewar shi, duk da yawan mutanen da suka mutu a cikin tashin hankali, dubun dubata sun tsira da rayuka a yau saboda sun samu mafaka a sansanonin MDD tare da samun taimakon da ya kamata. (Fatimah)