in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kaddamar da ranar tunawa da kisan kiyashin Rwanda
2014-02-28 13:03:51 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, ya jagoranci bikin kaddamar da ranar 7 ga watan Afirilun ko wace shekara, a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa kimanin mutane 800,000 a kasar Rwanda a shekarar 1994.

Yayin bikin na ranar Alhamis, wanda ya gudana a helkwatar majalissar dake birnin New York, Mr. Ban ya ja hankalin kasashen duniya da su kara himma, wajen aiwatar da tsare-tsare da za su karfafa darussan da aka koya, daga kisan kiyashin da ya auku a kasar ta Rwanda.

"Dole ne mu yi magana, da zarar mun lura cewa, wasu al'ummu, na fuskantar barazana daga masu nufin cin zarafinsu." a kalaman babban sakataren na MDD.

A cewarsa, bikin tunawa da wannan rana, da dubban al'ummar Rwanda suka rasa rayukansu bisa dalilai na kabilanci mai taken "Kwibuka 20", zai zamo wata hanya ta tunawa, da dinke baraka, tare kuma da sabunta halin da ake ciki a kasar, duka dai da nufin baiwa al'ummar kasar damar cimma burin sulhu mai dorewa.

Daga nan sai Mr. Ban ya nuna damuwarsa don gane da gazawar da kasashen duniya suka yi, wajen shawo kan rikicin kasar Sham a siyasance, da batun nuna wariya da wasu al'ummun yankunan Turai ke fuskanta, baya ga matsanancin halin da al'ummar Afirka ta tsakiya ke ciki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China